1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyyar Eu taki amincewa da bukatar kasar Russia akan kasar Iran

November 17, 2005
https://p.dw.com/p/BvKc

Kungiyyar tarayyar turai, wao Eu taki amincewa da tayin da kasar Russia tayi na daukar nauyin taron kolin kungiyyar da kasar Iran a game da kokarin da ake na warware zargin da akewa kasar na kokarin mallakar makaman nukiliya.

Kasar dai ta Russia ta gabatar da wannan shawara ne a yayin da saura kwanaki kadan a koma teburin shawarwarin a tsakanin wakilan kasashen Jamus da Biritaniya da kuma Faransa dake wakiltar kungiyyar ta Eu a hannu daya kuma da wakilan kasar ta Íran.

Kamfanin dillancin labaru na AFP dai ya rawaito cewa a mako mai zuwa ne ake sa ran komawa teburin shawrwarin a tsakanin wadan nan bangarori biyu a kokarin da ake na neman maslaha dangane da zarghin da akewa kasar ta Iran.

Idan dai za a iya tunawa an tashi daga irin wannan tattaunawa ne baran baran a daya ga watan Agusta, a lokacin da mahukuntan na iran suka shaidar da aniyar su taci gaba da sarrafa sanadarin na Uranium.

Bugu da kari kafin dai mahukuntan na Iran su yanke daukar wannan mataki sai da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya wato IAEA ta gargadeta da kada tayi hakan , amma kuma tayi kunnen uwar shegu da wannan gargadin.