kungiyyar Eu ta bayar da tallafin kudi don sake gina Libanon | Labarai | DW | 30.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

kungiyyar Eu ta bayar da tallafin kudi don sake gina Libanon

Hukumar zartarwa ta kungiyyar tarayyar turai, wato Eu tayi alkawarin ba da yuro miliyan 42, don sake gina kasar Libanon bayan yaki.

A cewar kwamishinan kungiyyar mai kula da harkokin ketare, wato Benita Ferrrero- Walder, hukumar zata gabatar da wannan tallafin ne a hukumance, a lokacin taron neman gidauniyar sake gina kasar ta Libanon.

Bugu da kari kwamishinan ya kara da cewa da cewa, kaso mafi tsoka daga cikin tallafin zai tafi ne ga bangaren bunkasa tattalin arzikin kasar.

A dai gobe alhamis ne ake sa ran gudanar da gidauniyar neman tallafin sake gina kasar ta Libanon, a birnin Stockholm na kasar Sweden.