Kungiyyar Eu na bukukuwan tunawa da ranar hadewar ya´yan ta | Labarai | DW | 09.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyyar Eu na bukukuwan tunawa da ranar hadewar ya´yan ta

A yau ne yayan kungiyyar Eu, ke gudanar da bukukuwan tunawa da ranar kafa kungiyyar hadin kann turan, wanda kasashen suka fara a kusan shekaru 20 da suka gabata.

Rahotanni dai sun nunar da cewa a shekara ta 1950 ne aka fara daukar matakan hade kann yayan kungiyyar ta turai, a karkashin laima daya.

A cikin wani jawabi data gabatar, shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci kungiyyar ta Eu data yi waiwaye, wanda hausawa kann ce adon tafiya don daukar matakan kara hade kann yayan kungiyyar, da nufin tunkarar kalubalen dake akwai.

Har ilya yau Shugabar Jamusawan ta tabbatar da aniyar ta na ci gaba da daukar matakin ganin an samar da kundin tsarin mulkin kungiyyar ta Eu, da aka dade ana cece kuce a kann sa.