1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyyar Au ta kusan samo bakin zaren

January 24, 2006
https://p.dw.com/p/BvAw

A wani lokaci ne a yau, wani dan kwarya kwaryar kwamiti da kungiyyarr Au ta kafa na nemo bakin zaren warware takaddamar shugabancin kungiyyar, yake mika mata rahoton sa.

A cewar daya daga cikin mammobin kwamitin ,wanda ya bukaci a sakaya sunan sa, ya shaidar da cewa rahoton ya shawarci kungiyyar ta Au data mika wannan shugaban ci izuwa kasar Congo, dake tsakiyar Africa.

Yin hakan a cewar kwamitin zai warware tababar da ake na mika wannan shugabanci a hannun kasar Sudan, Kasa da aka zarga da take hakkokin bil adama, musanmamma a yankin Darfur.

Bisa al´ada dai duk kasar da take daukar bakun cin taron , itace take karbar ragamar jagorancin kungiyyar na karba karba.

Kafin dai fara wannan taro na wuni biyua jiyav litinin, kungiyoyin kare hakkin bil adama sun shaidawa shugabannin kungiyyar na Au 53 cewa, bawa kasar ta Sudan wannan mukami ka iya dakushe kima da darajar kungiyyar a idon duniya, bisa irin yadda ake take hakkokin bil adama a yankin Darfur.