Kungiyoyyin yan tawaye sunki sanya hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya na Darfur. | Labarai | DW | 30.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyoyyin yan tawaye sunki sanya hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya na Darfur.

Kungiyoyin yan tawaye 2 da basa kaunar gwamnatin Sudan,sunki amincewa su sanya hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya na Darfur da Kungiyar Taraiyar Afrika ta tsara.

Wakilin JEM Ahmed Hussain yace basu amince da abinda yarjejeniyar ta kunsa ba,saboda haka ba zasu sanya hannu akai ba.

A nasa bangare wakilin SLM Saifaddin Haroun cewa yayi,yace zasu sanya hannu akan yarjejniyar ce idan ta cimma dukkan bukatunsu,amma ba wannan ba.

Kakakin kungiyar AU,Nourudeen Mezni yace,babu canji ga waadin da kungiyar ta yanke,haka kuma komitin sulhu yana goyon bayan wannan shiri,saboda haka a cewarsa,idan akwai wani bangare da bai sanya hannu kan yarjejeniyar ba,komitin sulhun ya san mataki da zai dauka.

Gwamnatin kasar Sudan dai ta baiyana amincewarta ga wannan yarjejeniya.