1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyoyin yan tawayen Sudan iyu sun ki amincewa da daftarin sulhu

Wa´adin da kungiyyar hadin kann kasashen Africa, wato Au ta bawa ragowar kungiyoyin yan tawayen nan na Sudan guda biyu ya kare a sha biyun daren jiya , wato wayewar garin yau, ba tare da kwalliya ta biya kudin sabulu ba.

Kungiyoyin yan tawayen dai sun ce ba zasu rattaba hannu akan kudurin zaman lafiyar da kungiyyar ta Au ta gabatar ba, har sai an gudanar da wasu yan gyare gyare a cikin kudurin.

Wadannan gyare gyare da kungiyoyin yan tawayen biyu ke muradin ganin an gudanar, ya bukaci basu karin yawan madafun iko ne , wanda a hannu daya kungiyyar Au da kuma gwamnatin Sudan suka ki amincewa da hakan.

Ya zuwa yanzu dai kungiyyar yan tawaye ta SLA da kuma gwamnatin Sudan ne kawai suka rattaba hannu akan amincewa da wannan kuduri.

Kafafen yada labaru sun rawaito kakakin kungiyyar ta Au, Nurudden Mezni na fadin cewa, matukar kungiyoyin yan tawayen basu amince da kudurin sulhun ba, to babu makawa zasu fuskanci fushin kwamitin sulhun kungiyyar ta Au.