Kungiyoyin yan gwagwarmaya a Palasdinu sunce zasu tsagaita wuta. | Labarai | DW | 24.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyoyin yan gwagwarmaya a Palasdinu sunce zasu tsagaita wuta.

Kungiyoyin yan gwagwarmaya a Palasdinu sun amince bisa kaida , tsagaita bude wuta da Israila.

Wannan sanarwa kuwa tazo ne bayan wata ganawarsu da Firaminista Ismail Haniyeh a Gaza.

Shugaban kungiyar Islamic Jihad Khader Habib ya fadawa manema labarai cewa yawancin wakilan kungiyoyn islama da sauran kungiyoyi na yankin sun gana da Haniyeh kuma sun amince da batun tsagaita wutar,muddin dai Israila itama ta amince .

Israilan dai nan take taki amincewa da wannan tayi,tana mai fadin cewa ba zata dakatar da aiyukan sojinta kann Palasdinwa ba har sai kungiyoyin sun ajiye makamansu.

Yanzu haka hare haren da Israila ta kaddamar a zirin Gaza tun ranar litinin sunyi sanadiyar mutuwar mutane 12 wasu kuma 20 suka jikkata.