KUNGIYOYIN SA KAI NA RASHA SUN YI MUHAWARA KAN MAKOMAR DIMUKRADIYYA A KASAR. | Siyasa | DW | 02.03.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

KUNGIYOYIN SA KAI NA RASHA SUN YI MUHAWARA KAN MAKOMAR DIMUKRADIYYA A KASAR.

A lokacin da shugaba Vladimir Putin ya hau karagar mulki kuma, ya yi alkawarin cewa, zai dinga tuntubar wadannan kungiyoyin kafin gwamnatinsa ta yanke wata shawara.

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin

Tun da kasar Rsaha ta rungumi tafarkin dimukradiyya, bayan wargajewar Tarayyar Soviet ne, aka yi ta kakkafa kungiyoyin sa kai, wato NGO a takaice a kasar. A halin yanzu dai, an kiyasci cewa, yawan kungiyoyin sa kan na Rasha, ya kai dubu 40 zuwa dubu 70.

Wasu daga cikin kungiyoyin dai, sun nuna damuwarsu ga yadda gwamnati ta mamaye yakin neman zaben kasar, wanda za a yi a cikin watan Maris mai zuwa, ta hana sauran jam’iyyun da ke hamayya da na gwamnatin sakewa, wajen gudanad da nasu kamfen din.

Ba da dadewa ba ne, kungiyar nan ta Heinrich-Boll ta nan Jamus ta shirya wani taro a birnin Berlin, inda mahalarta suka yi muhawara kan makomar dimukradiyya a kasar Rasha, da kuma irin rawar da shugaban kasar mai ci yanzu, Vladimir Putin, ya taka a fagen siyasa tun hawarsa karagar mulki, shekaru 4 da suka wuce. Jelena Schemkowa, daya daga cikin shugabannin kungiyar sa kan nan "Memorial" ta Rasha, ta halarci taron na Berlin. Game da yadda ake gudanad da yakin neman zabe a Rashan dai, ta bayyana cewa:-

"Mun dai lura cewa, kafin a yi zaben ma, an tabka magudi a tsarin shirye-shiryensa. Ban da keta dokokin zabe da ake yi a loakcin yakin neman zabe, a jihohi da ma a duk fadin kasa baki daya, mun kuma ga cewa ba a bin ka’idojin dimukradiyya. Kai majalisar kasar ma ba ta da wani ikon yanke wa kanta shawara, sai abin da gwamnati ta gabatar mata kawai ne take amincewa da shi."

Babu shakka, shugaba Putin dai ya mamaye duk madafan iko a kasar ta Rasha. Yana iya yin duk abin da ya ga dama, ba tare da wani ya kalubalance shi ba. Wani misali a zahiri a nan kuwa, shi ne rusa gwamnatin Firamiya Kasjanow da ya yi a kwanakin baya. Tun da aka yi zaben Majalisar dokokin kasar ta DUMA dai, fadar Kremlin ta sami cikakken rinjayi, ta yadda za ta iya sauya sassan kundin tsarin mulkin kasar kamar yadda ta ga dama. Jelena Schemkowa na ganin cewa, wannan halin kuwa, wani abu ne mai kawo damuwa a fagen siyasar kasar:-

"Jam’iyyar hadaddiyar Rasha da ke mulki, tana da rinjayi a majalisa, wanda za ta iya yin amfani da shi wajen sake kundin tsarin mulkin kasarmu. Abin ban takaici dai shi ne ganin yaddda tuni, wasu suka fara yunkurin aiwatad da canje-canjen. Shugaba Putin dai ya ce ba za a yi wa kundin wani garambawul ba. Amma duk da haka akwai masu tuntubar yin haka din. A halin yanzu dai, majalisarmu tana aiki ne kamar sakatariyar gwamnati. Gwamnatin ce ke tsara duk wasu dokoki, sa’annan `yan majalisar, wadanda suka zamo `yan amshin shatanta, su amince da su ba tare da yin muhawara a kansu ba. Hakan kuwa ya saba wa ka’idojin dimukradiyya a ko’ina ma."

A hankali dai, shugaba Putin, ya gurgunta duk muhimman kafofin siyasan kasar. Kazalika kuma, yana fatattakar duk masu yi masa suka ko kuma masu yunkurin kalubalantarsa a takarar zabe. Ta hakan ne dai, ya sa aka daure rikakken attajiri, dan kasuwar man nan, Michail Chodorkowski a kurkuku.

Jaridu da kafofin yada labarai masu zaman kansu ma ba su tsira karkashin mulkin Putin ba. Gwamnatinsa ta angaza wa da yawa daga cikinsu, har a wasu lokutan ma, ta rufe wasu da karfi da yaji. A lal misali a cikin watan Ifrilun shekara ta 2001, sai da gwamnati ta kwace gidan talabijin nan NTV, mai zaman kansa. Sa’annan a cikin watan Janairun shekarar bara kuma, ta rufe gidan talabijin nan TV6, mai yada shirye-shiryensa a duk fadin kasar. Har ila yau dai, wata daya bayan haka ne kuma gwamnatin Rashan ta angaza wa jaridar nan "Nowye Iswestia", har ta rufe kofofinta ta daina aiki.

Manazarta al’amuran yau da kullum dai na ganin cewa, wannan matakin daidai yake da haramta wa `yan jarida da maneman labarai gudanad da aikinsu a kasar ta Rasha.

 • Kwanan wata 02.03.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvla
 • Kwanan wata 02.03.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvla