Kungiyoyin musulmi na jamus sunyi Allah wadan harin bomb | Labarai | DW | 25.08.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyoyin musulmi na jamus sunyi Allah wadan harin bomb

Kungiyoyin musulmi mafi girma guda 16 dake tarayyar Jamus,sunyi Allah wadan harin Bomb wa jiragen kasa na pasinja guda biyu daya ci tura,a ranar 31 ga watan Yulin daya gabata.A sanarwar hadin gwiwa da suka gabatar ,kungiyoyin sun bayyana cewa wannan harin bashi da hujja a musulunce,kuma ayyukan taaddanci babban laifi ne daya sabawa addini da biladama baki daya.Sanarwar ta kara dacewa alumman musulmi dake nan jamus sun bayyana takaicinsu da wannan batu,domin ya shafesu a matsayin wadanda da wannan harin zai ritsa dasu,kana a daya hannun kuma ,mutane da dama zasu zargesu,saboda kasancewarsu musulmi.Kazalika kungiyoyin musulmin sunyi kira ga yan siyasa da kada suyi amfani da wannan dama waje ragewa jamaa yancinsu na walwala.

 • Kwanan wata 25.08.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5h
 • Kwanan wata 25.08.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5h