Kungiyoyi masu zaman kansu akan taron G8 | Siyasa | DW | 05.07.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kungiyoyi masu zaman kansu akan taron G8

Ƙungiyoyi masu zaman kansu sun jaddada bukatar karin tallafi wa Afrika

default

Angela Merkel da shugabar ƙasar Liberia, Ellen Johnson-Sirleaf.

Gabannin buɗe taron ƙasashe masu cigaban masana'antu na G8 ,shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gabatar da wani shiri na musamman wanda keda nufin kalubalantar matsalar karuwar farashin abinci,da bunkasa amfanin gona.

A gobe ne ake shirin kaddamar taron ƙasashe masu arzikin masana'antu na duniya da akafi sani da suna G8, a takaice a kasar japan.Gabannin bude wannan taro,Angela Merkel ta gabatr da muhimman batutuwa da taron zai mayar da hankali akai.

Taron na wannan shekara inji shugabar gwamnatin na Jamus,zai duba manyan matsaloli da duniya ke fama dasu,wadanda suka hadar da Dumamar yanayi,da tsadar abinci da Farashin mai da kuma taimakawa kasahen Afrika.

"Taron zai fara ne da ganawa ta musamman da shugabannin kasashe da gwamanatocin Afrika.Inda za a yi mahawara dangane da batun karuwar farashin mai da yadda za aiya shawo kan matsalar tsadar abinci."

Merkel tace taron zai duba hanyoyin da kasashe masu cigaban masana'antu zasu tallafawa kasashen na Afrika wajen bunkasa harkokin noma,ta yadda zasu ceto alummominsu.

Claudia dake kungiyar kula da tsarin taimakon raya kasashe na tarayyar jamus,dake zama kungiya mai zaman kanta, wannan batu ne dake da muhimmanci,kuma labari ne mai kyu wa waɗannan kasashe.

Idan aka kwatanta da shekara ta 200 dai,Kasashen na Afrika sun samu cigaba ta fannin ingantuwan tattalin arziki,kana an samu koma baya dangane da yawan mutanen da suke fama da matsanancin talauci,kana an samu karuwar yawan yara da suka samu shiga makarantu,domin samun ilimi na zamani,kazalika an samu cigaba ta fannin samar da magunguna wa wadanda ke fama da cutar AIDS.

To sai dai shugabar wannan kungiya tace duk da irin cigaba da aka samu,akwai matsaloli masu yawa da nahiyar ta Afrika ke cigaba da kasancewa dasu.Jamus dai cikin kasafin kudinta na shekara mai zuwa,ta kara yawan kudaden tallafin wa kasashe masu tasowa da wajen Euro million 800.

Claudia Warning tace dole ne kasashe masu cigaban masana'antu su mike tsaye,idan suna muradin ceto wannan nahiya daga halin da take ciki a yanzu.domin iya adadin tallafin da ake bayarwa baya isa ga kmatsaloli dake ɓulla sakamakon talauci.

"Idan aka kiyasta cewar, a yaki da cutar Aids ita kadai ,za a kashe tsakanin Dala billion 30 zuwa 40 a shekara,zamu san tsarin yadda za a kashe kudaden akaan sauran matsaloli,.Domin a kowace rana mutane dubu 24 ke mutu,saboda tsananin fatara da talauci"

A yanzu haka dai wannan kungiya ta taimakaw wani matashi ɗan kasar Togo ,Emmanuel Noglo ,wanda garinsu yake tazarar km 35 daga babban birnin kasar watau Lome,a yanzu kuma ya hade cikin wata kungiyar kirsitoci.

Emmanuel yace a garin su suna fama da matsalar karancin ruwan sha mai kyau.

"A karshen shekarun 1980,an sayar da hannayen jarin hukumar ruwan sha.A yanzu haka babu ruwansha mai kyau,domin babu inda mutum zai iya ganin run ma balle ya debo"

Matsalar karancin ruwan sha da wutan da samarda makamashi ,batutuwa ne muhimmai daya kamata kasashe masu cigaban masana'antu suyi la'akari dashi,wajen taimakawa kasashe mabukatu,musamman na Afrika,inji shugabar kungiyar mai zaman kanta,Claudia Warning...

"Muna da dukkannin abubuwanda ake bukata,da kudaden da zasu kunsa,domin ceto waɗannan al'umma,shine batu muhimmi daya rataya a wuyan kungiyar ta G8".