1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyoyi 40 a Africa sun soki lamirin kungiyyar Au

January 17, 2006
https://p.dw.com/p/BvBv

Kungiyoyi kusan 40 masu zaman kansu a nahiyar Africa, sun bukaci kungiyyar hadin kann kasashen Africa da kada su zabi shugaban kasar Sudan, Omar El Bashir a matsayin shugaban ta na gaba.

A cewar kungiyoyin dake da nasaba da fafutikar kare hakkil bil adama da shiga tsakanin warware rikice rikice, sun nunar da cewa rikon sakainar kashi da Shugaban kewa rikicin yankin darfur, na daga cikin dalilan daya tabbatar da gazawar shugaban na rike wannan mukami.

A cikin wata takarda da kungiyoyin suka aikewa shugabannin kungiyyar ta Au, sun fito karara sun nunar da cewa bawa Omar El Bashir ko kuma kasar ta Sudan wannan mukami, ka iya dakushe martaba da kimar kungiyyar a idon duniya.

Rahotanni dai sun nunar da cewa duk da balahirar take hakkin bil adama dake ci gaba da wanzuwa a yankin Darfur, a hannu daya kuma da sukar da akewa Omar El bashir na rikon sakainar kashi ga wannan rikici, ana hasashen cewa shugabannin kungiyyar ta Au na shirin bawa kasar ta Sudan wannan shugaban ci na tsawon shekara daya, bayan saukar shugaba Obasanjo na Nigeria.