1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar 'yan awaren ETA ta soma mika makamai

Gazali Abdou Tasawa
April 8, 2017

Mahukuntan kasar Faransa sun nuna gamsuwarsu da matakin bayyana wuraren ajiyar makamai da kungiyar 'yan awaren yankin Basque ta ETA ta yi a wannan Asabar.

https://p.dw.com/p/2avWm
ETA gibt Waffen ab
Hoto: Reuters/R. Duvignau

Mahukuntan kasar Faransa sun nuna gamsuwarsu da matakin bayyana masu wuraren ajiyar makamai da kungiyar 'yan awaren yankin Basque ta ETA ta yi a wannan Asabar a wani mani mataki na soma aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma a shekara ta 2011 wacce ta kawo karshen yaki na shekaru 43 da kungiyar ta share tana yi da kasar ta Faransa domin neman samun 'yancin kan yankin na basque. 

A halin yanzu dai 'yan sanda a kasar Faransa na can suna neman tantance mabuyar makamai guda takwas wadanda kungiyar ta ETA ta bayyana wa mahukuntan kasar. Ram Manikalingam na hukumar sa ido ta kasa da kasa kan shirin kwance damarar yakin Kungiyar ta ETA ya tabbatar da soma mika makaman yana mai cewa:

"Ya ce a yau wannan komiti ya gana da Jean Noel Etchevery wakilin kungiyoyin fararn hula na yankin Basque wanda ya gabatar da takardun shaidar wuraren buyar makaman, kuma tuni muka mika bayanan ga hukumomin faransa"

Tsohon Shugaban Hukumar kare hakkin dan Adam Michel Tubiana ya ce ana hasashen wuraren buyar makaman takwas na kunshe da bindigogi 120 da ton uku na ababe masu fashewa da dubunnan harsasai.