Kungiyar yaki da cin hanci zata karrama wasu jamiai a Nairobi | Siyasa | DW | 22.07.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kungiyar yaki da cin hanci zata karrama wasu jamiai a Nairobi

Shugaban kungiyar dake yaki da cin hanci da rashawa ta Transparency International Peter Eigen ya nuna damuwa ta yarda ake samun karuwar satar kudaden Gwamnati a kasashe masu tasowa .

default

Ga misali a can kasar Bangaladash wani babban Dan jarida Manik Chandara wanda yayi fice wajen tona asirin masu halayyar bera ya riski ajalinsa a farkon wannan shekarar da muke ciki a yayin da wasu sukai masa kisan gilla a cikin wannan gwagwarmayar na tabbatar da adalci a tsakanin alumma .A dangane da haka dai a yanzu gwamnatin kasar ta fara daukar sabbin matakai na kare ire iren wadannan jamiai domin kare mutuncin kasar baki daya musamman ga wadanda ke tona asirin jamian gwamnati ko kuma fannin masanaantu .Bugu da kari domin daukar wannan mataki a lokacin yana raye a yamnzu haka kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta AI zata karrama wannan mamacin a watan Oktoban wannan shekara a can Kasar Kenya .Kamar dai yarda daya daga cikin shugabannin wannan kungiya Sarah Tyler a berlin ta shaidawa kanfanin dillancin labarai na IPS cewa an dauki wannan mataki ne domin tabbatar da gudanar da gaskiya a tsakanin almumma tare da bayar da kwarin guiiwwa ga wadanda ke cigaba da tona wannan asiri har sai sun san cewa Gaskiya daya ce bata neman Ado ..Sarah dai tace a dangane da wannan halin ayanzu haka suna cigaba da samun wasiku dake jinjina masu bisa namijin kokari na fadakar da jammaa wannan illa ta satar kudaden jammaax ga wadanda ke rike da madafan iko a wadannan kasashe ..A cewar wannan jamiar dai tace a cikin wannan shekara an ware a kalla mutane 8 wadanda zasu karbi wannan lambar yabo wanda ukku daga cikin su Sun rigamu gidan Gaskiya .Cikin su kuwa har cda wani Injiniya dan Kasar Turkiyya Hassan Balik wanda ya mutu a shekara ta 2001.Shi dai hassan ya kasance wanda ya tona asirin wasu marasa imani wanda suka sace Miliyoyin kudade na kanfanin da yake aiki .Bugu da kari an zabi Farfesa Milica Bisuc wata Malama a jamiar Bosnia hezgobina ..WAta majiya na cewa tana daya daga cikin wadanda suka kwatanta tsoron allah a yayin da take rike da wata hukuma ta karbar haraji a kasar wanda kuma ta dauki matakin gudanar da gyare gyare ta wannan fanni .Kungiyar ta AI ta fitar da wadannan jamian ne cikin mutane 30 data tattara bayanai daga koina a cikin wannan Duniya domin wannan Lambar yabo .-Kwamitin dai dake aiki don cimma manufar nada wakilai 11 amintattu wadanda gaskiyarsu ta rinjayi karya ..Shugaban kungiyar yaki da cin hanci da rashawa a duniya dake da mazauninta a nan jamus a Berlin Peter Eigen ya tabbatar da karuwar satar kudadfen Talakawa a duniya baki daya wanda ya bukaci .Jamian da zasu karbi wadannan lambobi sun hadar da Satyandra Kumar dan Kasar India Lother hames Bajamushe Grigoris Lazos daga Girka David Munyaki da Naftali yan kasar Jkenya .Duka dai wadannan jamian sun tona wata badakala ce a lokuta daban daban wanda kudasden suka tasamma Miliyoyin kudade .A dangane da haka ne kungiyar ta yaki da cin hanci da rashawa taga ya dace ta karrama su domin ya zama misali ga yan baya

 • Kwanan wata 22.07.2004
 • Mawallafi Mansour Bala Bello
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvhq
 • Kwanan wata 22.07.2004
 • Mawallafi Mansour Bala Bello
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvhq