1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar WHO ta ce ana iya amfani da maganin kashe kwari na DDT

September 16, 2006
https://p.dw.com/p/BujS

Kungiyar lafiya ta duniya WTO ta yi kira ga kasashe masu tasowa musamman na Afirka da su fara feshin maganin kashe kwari na DDT wato hodar kwari ko garin aya a cikin gidaje, a wani mataki na yaki da zazzabin cizon sauro wato malaria. An dade da haramta yin amfani da hodar kwarin wato DDT a Amirka da kuma wasu kasashe saboda lahanin da yake yiwa kewayen dan Adam. To amma daraktan kungiyar ta WTO, Dr. Arata Kochi ya ce maganin na DDT na da inganci kuma bai da wani lahani idan aka yi amfani da shi a cikin gidaje musamman idan aka fesa shi kan shara. A duk shekara zazzabin cizon sauro na halaka mutane kimanin miliyan daya daukacin su kananan yara ´yan kasa da shekaru 5 na haihuwa.