Kungiyar Turai tace ba ja da baya ga batun mika Mladic | Labarai | DW | 13.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Turai tace ba ja da baya ga batun mika Mladic

Jamian Kungiyar Taraiyar Turai sunce basu da aniyar dage waadin karshen wannan wata da suka baiwa Serbia ta mika janar Ratko Mladic bayan mutuwar Slovadan milosevic.

Mai magana da yawun kungiyar Kriztina Nagy tace babu wani sauyi a matakan da suka rigaya suka dauka game danganta mika Mladic da shigar Serbia cikin kungiyar .

Nagy ta gargadi magoya bayan Mladic da kada suyi anfani da batun mutuwar Milosevic su ki mika Mladic wanda kotun MDD take zargi da alhakin kashe maza manya da yara 8,000 musulman Bosnia.

Tace dole ne shugabannin Serbia su bada hadin kansu da kotun kasa da kasa dake sauraron laifukan yaki.