Kungiyar tawayen LRA a Uganda ta gayyaci gwamnati zuwa shawarwarin sulhu | Labarai | DW | 30.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar tawayen LRA a Uganda ta gayyaci gwamnati zuwa shawarwarin sulhu

A kasar Uganda mataimakin shugaban kungiyar tawaye ta LRA,ya sanar cewa, kungiyar a shire ta ke ta hau tebrin shawarwari, da gwamnati, da nufi kawo karshen yakin bassaka na tsawon shekaru 19 da ya daidaita wannan kasa.

Vincent Otti, da ke magana da yawun shugaban LRA, ya karyata zargin da gwamnati ke yi wa kungiyar ta su, da kai hare hare ga jami´an kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa, da ke aiki a arewancin Unganda.

A game da bukatar gurfanar da shugabanin kungiyar tawayen gaban kotun Kasa da kasa, ta birnin The Hage, ko kuma La Haye, ya ce shire ya ke, ya amsa kiran wannan kotu,amma da sharadin gurfana tare da gwamnatin Uganda, wadda itace, ke hadasa ruruwar wutar rikicin kasar, a cewar sa.

Yakin bassasa da ke gudana a arewancin kasar Uganda, ya yi sanadiyar mutuwar dubunan mutane, a yayin da kussan wasu million 2 su ka shiga uwa dunia.

A yayin da ta ke maida martani ga wannan kira, na yan tawaye gwamnatin kasar ta bayana cewa wasa ne da hankali, su ke yi badan kamai ba pace, su yi yaudari dakarun gwamnati.