Kungiyar Tariyar Turai tayi maraba da sabuwar gwamnatin Palasdinwa | Labarai | DW | 18.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Tariyar Turai tayi maraba da sabuwar gwamnatin Palasdinwa

Kungiyar Tariyar Turai tayi maraba da rantsar da sabuwar gwamnatin hadin kann Palasdinawa data hada da kungiyar Hamas da Jamiyar Fatah ta shugaba Mahmud Abbas.

Sai dai kasar Jamus wadda ke rike da shugabancin kungiyar tace zata sa ido akan yadda sabuwar gwamnatin zata gudanar da aiyukanta,kafin ta yanke shawara kann sake maida taimakonta ga Palasdinawan.

Kasashen Amurka da Israila sunce ba zasu yi hulda da sabuwar gwamnatin batunda har yanzu Hamas tana kann bakarta ta kin amincewa da Israila.

Kakakin maaikatar harkokin wajen Amurka Sean McCommack yace abin takaici ne kalaman da Haniyeh yaiwa majalisa cewa suna da ikon jajircewa duk wani yunkuri na adawa dasu.

Firaminista Haniyeh a nashi bangare yace ya kamata kasashen Isarial da Amurka suyi laakari da cewa akwai wadanda suka amince da Israila cikin ministocin Palasdinu.