Kungiyar Tarayyar Turai (KTT) Zata Fara Shawarwarin Karbar Turkiyya
December 17, 2004Bisa ta bakin P/M Turkiyya Tayyib Erdogan dai har yau da sauran rina a kaba, domin kuwa kamar yadda majiyoyi masu nasaba da mashawartan Turkiyyar suka nunar, kasar ba zata yarda da amincewa da ikon cin gashin kan bangaren Girkawa na tsuburin Cyprus, a matsayin sharadin gabatar da shawarwarin karbarta a Kungiyar Tarayyar Turai ba. Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder, wanda ke ba da cikakken goyan baya ga karbar Turkiyyar a Kungiyar Tarayyar Turai bayan shekara ta 2014, ya bayyana fatan cimma bakin zaren warware matsalar ta Cyprus. A lokacin da yake bayani Schröder karawa yayi da cewar:
Maganar, a hakika, ba ta shafi amincewa da Cyprus ba ne a hukumance, batu ne da ya shafi shigar da ita a yarjejeniyar fito dake tsakanin Turkiyya da KTT. A saboda haka na sikankance cewar za a samu wata kafa, wacce zata gamsar da dukkan bangarorin biyu.
A taron kolinsu da suke gudanarwa yanzu haka a Brussels, shuagabannin kasashen Kungiyar ta Tarayyar Turai, sun amince da fara shawarwarin karbar Turkiyya a tutar kungiyar da kuma karfafa dangantakar kasar idan har shawarwarin, wadanda za a tafiyar da su ba tare da fayyace ainifin sakamakonsu ba, ba su cimma nasara akan manufa ba. Wannan bayanin ko da yake ya gamsar da ‚yan mazan-jiya dake dari-dari da karbar Turkiyyar a KTT, amma ita kanta kasar ta yi kakkausan suka game da shi, da kuma shawarar kungiyar na kayyade yawan ‚yan ci rani Turkawa da za a kyalesu su rika neman aiki a sauran kasashenta bayan karbar Turkiyyar. Tuni dai P/M kasar Sweden Gunnar Persson ya gargadi Turkiyyar a game da neman wuce gona da iri a bukatun da take neman shimfidawa. A sakamakon kai ruwa ranar da aka sha famar yi a game da kasar ta Turkiyya, ba a mayar da hankali sosai ga ganawar da aka shirya tsakanin sakatare-janar na MDD Kofi Annan da shuagabannin kasashen KTT ba, inda zasu tattauna manufofin hadin kai da ma’amalla tsakanin sassan biyu. An dai shiga yada jita-jita a game da ko shin Kofi Annan zai iya shiga tsakanin domin shawo kan matsalar ta Cyprus. A cikin watan afrilun da ya wuce ne Girkawan Cyprus suka yi fatali da shawarar da Kofi Annan ya bayar na sake hadewar tsuburin bayan rarrabuwa ta tsawon shekaru 30, a yayinda a daya bangaren Turkawan tsuburin suka amince da shawarar tasa.