1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Tarayyar Turai da Chadi

Ahmad Tijani LawalFebruary 6, 2008

Sharhi kan rikicin Chadi da manufofin turai

https://p.dw.com/p/D3aP
Dakarun gwamnati a Ndjamena.Hoto: AP
Bisa ga dukkan alamu dai shugaba Idris Deby na ƙasar Chadi ya sake tsallake rijiya da baya, daidai da abin da ya faru a shekara ta 2006. Domin kuwa an samu kafar karya alkadarin 'yan tawaye, wadanda suka kutsa N'Djamena kuma tuni suka bayyana shirinsu na tsagaita wuta. Ita ma Faransa, wadda tayi wa Chadi mulkin mallaka, ga dukkan alamu, bata da ra'ayin kawo karshen shugabancin Deby, saboda tuni shugaba Sarkozy yayi masa tayin taimako, a yayinda ita kuma Kungiyar Tarayyar Turai take fatan tsugunar da dakarunta a gabacin Chadi. Thomas Mösch daya rubuta wannan sharhi ya ce, ba wani abin mamaki a game da abubuwan dake wakana a ƙasar Chadi yanzu haka kuma za a ci gaba da fuskantar wadannan matsaloli matsawar da madafun ikon kasar ke hannun wata gwamnati da kasashe ko kuma wasu kafofi na kasa da kasa ke amfani da ita domin cimma bukatunsu. Ita dai Faransa bata taba ba wa Chadi cikakken ikon cin gashin kanta ba, a yayinda ita kuma Kungiyar Tarayyar Turai ke ba wa Faransar wata cikakkiyar dama ta cin karenta babu babbaka a kasar ba tare da ba da la'akari da manufofi na demokradiyya ko kiyaye hakkin dan-Adam ba. A daya bangaren kuma kwatar mulki da karfin hatsi ba zai tsinana wa talakawan ƙasar ta Chadi kome ba, saboda rikicin na wakana ne tsakanin wasu tsiraru 'yan gata da suka dade suna gwagwarmayar kama madafun iko tsakaninsu tare da watandar da arzikin da Allah Ya fuwace mata. Shi kansa Idris Deby ya isa zama kyakkywan misali a game da manufofin kasar Faransa. A shekara ta 1990 ne ya dare kan karagar mulki ta hanyar da tsaffin kawayensa kuma abokan adawar na yanzu ke fafutukar yin amfani da ita. Daga bisa ni Deby, bayan cimma daidaituwa da Faransa, ya gabatar da wata kwaryakwaryar demokradiyya. A kuma misalin shekaru uku da suka wuce yayi wa daftarin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin sake tsayawa takarar zaben da ya lashe tare da magudi. Wani abin lura a game da wannan famar kai ruwa rana da ake yi shi ne kasancewar Chadi a cibiyar Afurka take kuma a sakamakon haka ta zama wani muhimmin dandalin sojan Faransa a wannan nahiya. A baya ga haka a 'yan shekarun da suka wuce kasar, dake daya daga cikin kasashe 'yan rabbana ka wadata mu, ta wayi gari a cikin jerin kasashe masu arzikin mai. Shugaba Deby ya samu kafar shawo kan kasashen Kungiyar Tarayyar Turai da Amurka domin tafiyar da huldar cinikin mai salin alin ba tare da wata tangarda ba. Kuma tuni shugaban ya sa kafa yayi fatali da yarjejeniyar da aka cimma da bankin duniya a game da bai wa talakawan Chadi wata dama ta cin gajiyar arzikin man. Wani abin da ya zame wa Deby tamkar gobarar titi kuma shi ne rikicin lardin Darfur na kasar Sudan. Domin kuwa a yanzun zai samu rufa baya daga sojojin kungiyar tarayyar Turai, wadanda aka fara tsugunarwa domin ba da kariya ga 'yan gudun hijirar Darfur a Chadin. A takaice dai ko da yake bayyanarwa a fili da kungiyar tarayyar Afurka da kuma kwamitin sulhu na Majalisar Ɗunkin Duniya suka yi cewar ba za a amince da kwatar mulki da karfin bindiga a kasar ta Chadi ba, amma a daya bangaren kuma wajibi ne Faransa da Kungiyar Tarayyar Turai sun ankara da gaskiyar cewa cimma wata manufa mai sassauci da raba madafun mulki shi ne zai samar da zaman lafiya da kwanciyar mai dorewa a kasar dake tsakiyar nahiyar Afurka.