1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Taraiyar Turai ta soke shirin tattaunawa da Rasha

November 24, 2006
https://p.dw.com/p/BuaY

Kungiyar Taraiyar Turai ta soke shirin fara wata tattaunawa kan batun kirkiro da harkokin hadin kai da Rasha bayan kasar Poland ta dare kujerar naki game da fara wannan tattaunawa.

Kungiyar dai tana fatar fara wannan tattaunawar ce wajen babban taronta da zata fara yau a Helsinki.

Kasar Poland tayi karan tsaye ne game da wannan batu a matsayin martani kan takunkumin da Rasha ra dora kann shiga da nama da kayan lambu daga kasar Poland zuwa Rashan.

Kasar Poland itace kasa ta farko cikin kungiyar ta turai data taba yin nafani da ikonta na darewa kujerar naki game da wata tattaunawa da wata kasa.

Kungiyar Tariayar Turai ta dade tana neman cike gibin banbance banbance dake tsakaninta da Rasha kan yadda zaa tabbatr da ci gaban samarda mai da iskar gas,hakazalika da batutuwan demokradiya da kare hakkin bil adama.