1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar taraiyar Turai ta kira taron gaugawa akan batun iskar gas tsakanin Rasha da Ukraine

December 30, 2005
https://p.dw.com/p/BvES

Kungiyar Taraiyar Turai ta kira taron gaugawa na jamian makamashi na kasashe membobi a ranar 4 ga watan janairu mai kamawa,saboda tsoron katsewar samarda iskar gas sakamakon rikici tsakanin Rasha da Ukraine.

Kakakin hukumar Turai,Amedou Altafaj Tardio,yace an kira taron ne domin shiryawa duk wani abu da ka iya tasowa,da kuma yadda zaa fuskanci lamarin tare.

Kungiyar Taraiyar Turai dai tana sayen kashi 25 cikin dari na iskar gas dinta daga kanfanin Gazpom mallakar Rasha,kuma yawanci suna bi ne ta bututun kasar Ukraine.

Kanfanin yayi barazanar katse samarda gas zuwa Ukraine har sai ta amince da karin farashin iskar gas din ,wanda ya sanya kasashen Taraiyar Turai suke ganin zai shafi nasu iskar gas da suke samu.