1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Taraiyar Turai ta janye batunta na kaiwa kasar Iran Majalisar Dinkin Duniya

Hauwa Abubakar AjejeSeptember 22, 2005

Kasashen Burtaniya,Faransa da Jamus,sun dakatar da batunsu na kaiwa kasar Iran gaban komitin sulhu,yayinda kasar Rasha take nuna adawa akan wannan batu.

https://p.dw.com/p/BvZT
Shugaban Kungiyar Taraiyar Turai,Emmanuel Barroso
Shugaban Kungiyar Taraiyar Turai,Emmanuel BarrosoHoto: AP

A farkon wannan mako ne dai Kungiyar Taraiyar Turan take ta yin kira da a kai kasar Iran gaban komitin sulhu na majalisar dinkin duniya,akan shirinta na nukiliya wadda kasar Amurka take zargin cewa shiri ne na kera makaman kare dangi a boye.

Sai dai kuma wasu kasashe membobin hukumar gudanarwar,hukumar sa ido kan yaduwar makaman nukiliya ta kasa da kasa da suka hada da Rasha,Sin da kasashe yan ba ruwammu,sunyi adawa da daukar mataki mai tsanani akan Iran,suna masu baiyana cewa saka takunkumi akan Iran zai kara dagula alamura ne ko kuma ya samu martani mai zafi daga kasar ta Iran mai arzikin man fetur.

Shawarar da yanzu hukumar ta yanke itace,cewa darektan hukumar, Muhammad Elbaradei ya mika rahoton aiyukan nukiliya na Iran ga hukumar gudanarwa ta hukumar sa ido kan makaman wadda ita kuma zata duba ta rubuta nata rahoto da zata mikawa komitin sukhu domin daukar mataki daya dace akan Iran.

Hukumar,a taron nata,ta zargi Iran da laifin saba yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya,wadda take memba cikinta.

Wani jamiin diplomasiya wajen taron yace,shawarar da Kungiyar ta Turai ta yanke na dakatar da batun kaiwa karar Iran din cikin wannan mako,ya biyo bayan adawa mai karfi da kasar Rasha ta nuna ne game da batun.

Kodayake baa tabbatar ko wannan shawara zata samu karbuwa wajen kasar Rasha da sauran kasashe yan baruwammu ba,yayinda kungiyar take ci gaba da taron nata a yau alhamis.

Wani jamin na diplomasiya kuma cewa yayi wannan shawara ta Kungiyar Taraiyar Turai, wani koma baya ne,ganin cewa manyan kasashe uku na kungiyar wato,Burtaniya,Faransa da Jamus,sun mika wani kuduri mai karfi da yayi kira da a gaggauta daukar mataki kan Iran,yanzu kuma suna neman a dakatar da batun har sai a taron sun a gaba.

Wasu jamian na diplomasiya kuma suna ganin cewa,rashin cimma matsayi guda akan batun nukiliya na Iran zai rage zafin barazana da kasashen suke nemen yiwa kasar Iran din ne domin ta ji tsoro ta janye daga aiyukanta na nukiliya.

Wani jamin Amurka ya fadawa kanfanin dillancin labari na AFP a Washington cewa,ya tabbata Amurka da kawayenta zasu samu nasara idan an jefa kuria akan batun sakawa Iran takunkumi domin a cewarsa,kasashe 18 cikin kasashe 35 membobin hukumar suna goyon bayan Amurka.

Wani jamiin na diplomasiya kuma na wata kasa yar baruwanmu da bai yarda an baiyana sunansa ba cewa yayi,mataki da Amurka da kawayenta suke son dauka yayi zafi ainun, kuma yana ganin wani martani ne ga jawabin da shugaban kasar iran yayiwa taron Majalisar Dinkin Duniya ne a ranar asabar da ta gabata,inda yace kasar Iran tana da yancin samarda fasahar nukiliya na zaman lafiya, yana mai yin watsi da kiraye kiraye na dakatar da sarrafa sinadarin Uraniyum,ta yadda zaa iya anfani da shi wajen samarda sinadarin kera makamin kare dangi ko kara karfin tashoshin nukiliya.

Kasashen na Turai sun baiyana aniyarsu ta sassautowa game da wannan batu,suna masu bukatar goyon bayan kasar Rasha wadda take da ikon darewa kujerer naki a hukumar.