Kungiyar taraiyar Turai ta bullo da sabbin matakan kare taadanci | Labarai | DW | 02.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar taraiyar Turai ta bullo da sabbin matakan kare taadanci

Ministocin sharia dana harkokin wajen Kungiyar Taraiyar Turai a yau sun amince da sabbin tsare tsare na adana bayanai na sadarwa a kokarinsu na yaki da taaddanci.

Ministar sharia ta Denmark Lene Espersen ta fadawa kanfanin dillancin labarai na Reuters cewa,wannan yarjejeniya wani muhimmin mataki ne na tilastawa kanfanonin sadarwa na kasashe 25 na kungiyar ta turai domin su rika adana duk kanin maganganu da akayi ta wayar tarho ko ta hanyar yanar gizo domin gano masu tsatsauran raayi.

A nan gaba cikin wannan wata ne ake sa ran majalisar turai zata amince da wannan shawara.