1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Taraiyar Turai ta alkawarta sa baki a rikicin Darfur

Hauwa Abubakar AjejeOctober 12, 2005

Kungiyar ta Turai,tare da majalisar dinkin duniya suna ci gaba da ganin an kawo karshen rikici da kuma matsaloli da suke shafi yankin Darfur.

https://p.dw.com/p/BvYr
Javier Solana a Darfur
Javier Solana a DarfurHoto: AP

Kungiyar Taraiyar Turai tace zata matsawa bangarorin dake rikici da juna a yankin Darfur lamba ta hanyar siyasa,har sun kawo karshen rikicin.

Ministan harkokin waje na Kungiyar,Javier Solana,yace dole ne yan tawaye da kuma gwamnatin sudan su nemi hanyoyin siyasa na magance matsalar dake tsakaninsu.

Rikicin Darfur tsakanin bakar fatar Darfur da kungiyar da gwamnati ke marawa baya ta janjaweed tun 2003,yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla dubu 30 wasu kima miliyan biyu suka tagaiyara.

Solana yace ya kamata bangarorin biyu su sani cewa,ba zaa cimma nasara ba ta yin anfani da karfin soji a wannan rikici,yace hanya da ake bukata yanzu itace tattaunawa ta hanyar siyasa domin kawo karshen wannan takaddama.

A halin yanzu kungiyar hada kan Afrika tana da dakarunta 6300 daga kasashen Rwanda,Nigeria,Senegal,Afrika ta kudu da Gambia, wadanda suke sa ido kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin yan tawaye da kungiyar janjaweed.

A halin da ake ciki kuma,mai bada shawara ta musamman ga majalisar dinkin duniya akan wadanda suka tagaiyara,Dennis McNamara, yace,ya kamata kasashen duniya su inganta kokarinsu da suke na taimakawa miliyoyin mutanen da suka rasa matsugunansu sakamakon yakin basasa na kasar Sudan ko kuma a sake fuskantar barazanar tashe tashen hankula a kudancin kasar.

Yace babu isassun kudi da zasu taimaka sake tsugunar da wadannan mutane,yana mai kira ga masu bada gudumowa da su kara yawan abinda suke bayarwa domin kare wasu matsaloli kuma.

Kimanin mutane miliyan 4 suka rasa matsugunansu a kudancin Sudan,saura kuma daga Darfur,a yammacin kasar inda wani rikicin na dabam barke tun shekarar 2003.

Sai dai abin da jamaa suke fata anan shine,yan kuduncin kasar zasu koma gida sakamakon yarjejeniyar da aka rattabawa hannu tsakanin gwamnatin Khartoum da tsohuwar kungiyar yan tawaye ta SPLM a watan janairu da ya gabata.

Tun a lokacinda aka kafa wancan yarjejeniya,wadda ta kawo karshen yaki da aka fara tun 1983 lokacinda kiristoci da majusawa na kudancin Sudan suka kaddamar da yaki akan musulman arewacin kasar,mafi yawa na jamaar kudancin kasar sunyi takakka zuwa kauyukansu,inda suke taradda an lalata komai da komai.

Majalisar Dinkin Duniya tace,dubub dubatar mutane sun rigaya sun koma gidajensu,ana kuma sa ran fiye da rabin miliyan kuma zasu bi baya cikin yan watanni masu zuwa.

McNamara yace,mafi yawa na yankunan yanzu babu isasshen rowan sha,matsuguni,da kuma magunguna da sauran ababen more rayuwa.

Yace ba zaa dai ce wannan babban balai ba ne,to sai dai yana cike da hadari ,ya kara da cewa,nan bada jimawa ba Majalisar Dinkin Duniya zata kaddamar da asusun neman taimako na dala miliyan 48 domin taimakawa mutanen da suka koma kauyukan nasu.