Kungiyar Taraiyar Turai ta alkawarta karin kudi ga wadanda fari ya shafa a Afrika | Labarai | DW | 08.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Taraiyar Turai ta alkawarta karin kudi ga wadanda fari ya shafa a Afrika

Kungiyar Taraiyar Turai a yau ta alkawarta karin dala miliyan 6 na agajin gaggawa ga miliyoyin jamaa da fari ya shafa a kasashen Kenya Somalia,da Habasha,kuma tace zata kebe dala miliyan 48,idan halin da ake ciki ya kara tsananta.

Hukumar turai tace,zaa yi anfani da kudaden ne wajen samarda ruwan sha, abinci da kiwon lafiya ga mutane miliyan 5 da dubu dari hudu na kasashen yankin kahon Afrika.

Komishinan raya kasashe na kungiyar Louis Michel,yace balain yunwa na yiwa jamaar yankin barazana,muddin dai kasashe masu bada gudumowa basu taimaka cikin gaggawa ba.

Tun da farko kungiyar taraiyar turai ta bada dala miliyan 87 domin taimaka rage matsalar fari a yankunan na Afrika.