1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Taliban a kasar Pakistan ta fidda wata sanarwa

Zulaiha Abubakar
February 12, 2018

Kungiyar Taliban a kasar Pakistan ta tabbatar da mutuwar mataimakin shugaban kungiyar tare da sanar da nadin Mufti Noor Wali a matsayin wanda zai maye gurbinsa .

https://p.dw.com/p/2sWue
Taliban Angreifer Schule in Peschawar
Hoto: Reuters/Pakistan Taliban

Kungiyar ta kuma kara da cewar Noor Wali zai c igaba da jagorantar 'yan kungiyar Taliban  da ke kudancin Waziristan yankin da ke da manyan tsaunika kuma sansanin 'yan ta'adda da ke kan iyakar kasar Afghanistan. Har yanzu dai Sojojin Kasashen Amirka da Afganistan na ci gaba da zargin Pakistan da ba 'yan ta'adda mafaka duk kuwa da cewar Pakistan na cewa kage ake yi ma ta.