Kungiyar Red Cross ta mika kokon baranta na dala miliyan 300 | Labarai | DW | 30.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Red Cross ta mika kokon baranta na dala miliyan 300

Kungiyar agaji ta duniya redcross ta mika kokon baranta na neman taimakon dala miliyan 300 cikin domin taimakawa kasashe shiryawa balaoi na canjin yanayi da cutar kanjamau cikin wannan shekara.

Kungiyar ta kasa da kasa tace canjin yanayi wanda masana kimiya suka sanarda da cewa zai iya haifar da mummunar illa ga muhalli,wadanda suka hada da ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwa,musamman a kasaseh matalauta.

Sakatar janar na kungiyar Markku Niskala ya sanarda da cewa wadanda suke fuskantar wannan barazana sun hada da tsofi da marasa karfi da kuma matalauta,saboda haka dole ne a yi tanadi na taimakawa wadannan mutane.

Hasashen kididiga da akayi sun nuna cewa cutar kanjamau zata kashe mutane fiye da yadda yaki balaoi da annoba suka halaka mutane cikin shekaru 50 da suka shige a koina cikin duniya.