Kungiyar Oxfam ta jaddada kiran tallafawa yakin gabancin Afrika da taimakon abinci | Labarai | DW | 23.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Oxfam ta jaddada kiran tallafawa yakin gabancin Afrika da taimakon abinci

Ƙungiyar bada agaji ta Oxfam, ta soki lamirin ƙasashe masu da hannu da shuni, da ƙungiyoyin bada agaji na ƙasa da ƙasa, a kan kunnen uwar shegu da su ka yi, bayan kiran da a ka yi masu, na kai taimakon gaggawa ga wasu yankuna na Afrika ta gabas, da ke fama da matasalar yinwa.

ƙungiyar Oxfam, ta bayyana cewar daga jimmilar kuɗaɗe Dalla million 574, da a ke bukata domin tallafawa ƙasashen, a halin yanzu an samu kashi 32 bisa 100 kawai.

A ƙalla, mutane million 11 ne, daga ƙasashen Ethiopia Kenya da Somalia, ke bukatar tallafin gaggawa.

Kakakin hukumar Oxfam yayi kira ga wakili mussamman na Majalisar Dinkin Dunia, da ke ziyara a halin yanzu a wannan yanki, a game da wajibcin ɗaukar mattakan da ya dace a lokacin da ya dace don gudun ayi gociya bayan mari.