Kungiyar OSCE sun fara taro a Madrid | Labarai | DW | 29.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar OSCE sun fara taro a Madrid

Fiye da ministaoci 40 daga ƙasashe 56 na ƙungiyar Tsaro da Haɗin kai a turai, ko kuma OSCE, sun fara taro a Madrid, babban birnin Spain. Batun barazanar da ƙasar Rasha tayi na shirin janye kanta daga wata yarjejeniya da ta hana bazuwar makamai cikin duniya, shine zai fi daukan hankali a zauren taron. Rasha tace zata janye kanta daga wannan yarjejeniyar daga ranar 2 ga watan disamba, domin nuna adawa game da shirin Amurka na girka kafar kariya na nukiliya a gabacin turai. Kana, mahallarta taron zasu duba yiwuwar shigar da Kosovo tare da ƙara faɗaɗa ƙungiyar, bayan shekarar ta 2007.

ƙasar Spain ce ke shugabancin ƙungiyar tsaron na EU a yanzu haka.