Kungiyar OIC ta zargi gamaiyar kasa da kasa da rashin daukar matakan kawo karshen rikicin Lebanon | Labarai | DW | 03.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar OIC ta zargi gamaiyar kasa da kasa da rashin daukar matakan kawo karshen rikicin Lebanon

Kungiyar kasashen musulmi ta duniya wato OIC, wadda ke gudanar da wani taro a Malaysia, ta bukaci da a tsagaita wuta nan take a rikicin Lebanon. Kungiyar ta kuma nunar da cewa tana nazarin kafa wata rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasashen musulmi wadda za´a a girke ta a kudancin Lebanon. Mahalarta taron na musamman wanda Malaysia ke karban bakoncinsa sun ce zasu bukaci da girke rundunar ta musulmi amma a karkashin kulawar MDD. Kasashen kungiyar ta OIC sun soki lamirin gamaiyar kasa da kasa na yin munafunci a rikicin na Lebanon. Kungiyar ta ce zata yi kira da a gudanar da bincike na kasa da kasa akan laifukan yaki da ake zargin Isra´ila da aikatawa a cikin Lebanon da kuma Zirin Gaza.