Kungiyar musulmi ta duniya OIC ta shirya taimakawa gwamnatin Hamas | Labarai | DW | 20.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar musulmi ta duniya OIC ta shirya taimakawa gwamnatin Hamas

Firaministan kasar Malaysia,Abdullah Badawi,yace,kungiyar kasasen musulmi ta duniya OIC ta shirya yadda zata rinka bada taimakon agaji da na kudi ga hukumar Palasdinwa karkashin mulkin kungiyar Hamas,yayinda yake suka ga Amurka da Israila da suka yanke taimakon kudi da suke baiwa hukumar Palasdinawa.

A hira da kanfanin dillancin labarai na AFP ,firaministan na Malaysia wanda ke shugabantar kungiyar kasashen musulmi a yanzu,yace tuni ya tattauna da wasu shugabannin kungiyar game da wannan taimako,yace abin mamaki ne cewa kasar Amurka dake tilastawa kasashen duniya bin tafarkin demokradiya,sai gashi yanzu ta gagara amincewa da sakamakon zaben yankin Palasdinu,tare da dakatar da taimakawa hukumar Palasdinu karkashin kungiyar Hamas.

Yace bai gane da irin manufofin Amurka ba,kuma ya kamata jamaa su amince da zabin Palasdinawa,tunda a cewarsa suna tsammanin kyakyayawan shugabanci daga bangaren kungiyar Hamas.

Yace Plasadinwa sun dade suna cikin wahala ya kamata a basu damar zama cikin kwanciyar hankali a wannan karon.