Kungiyar limaman Chochi ta duniya ta ce zata kwashe jarinta daga kamfanonin dake goyon bayan Isra′ila-- | Siyasa | DW | 21.10.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kungiyar limaman Chochi ta duniya ta ce zata kwashe jarinta daga kamfanonin dake goyon bayan Isra'ila--

Isra'ila bata ji dadin matakin da kungiyar malaman Chochi ta duniya ta dauka ba--

default

A yanzu haka dai reshen wata babar chochi ta kasa da kasa dake Amurka ta yi barazanar dakatar da daina zuba jairinta cikin kamfanonin dake goyon bayan mamayewar da sojin Isra’ila ke yiwa yankunan cin gashin kann Palasdinawa,inda ta ce zata cigaba da tsayawa kann wanan mataki da suka dauka duk kuwa da cewar Isra’ila bata ji dadin wanan mataki da Chochin ta kasa da kasa ta dauka ba,kamar yadda wanan sanarwar ta fito daga wasu kungiyoyin yahudawa da kuma wasu yan majalisar datijan Amurka.

Chochin dai ta kasa da kasa ta Amurka mai suna General Assembly of Presbyterian ta manyan limaman Chochi ta duniya,ta ce zata dauki matakan da suka dace cikin tsare tsarenta na dakatar da yin wata hulda da kamfanonin dake goyon bayan mamayewar da Isra’ila ta yiwa yankunan Palasdinawa.

Reverend William Somplatsky –Jarman dake shugabantar kwamitin dake lura da zamantakewa da sharia na Chochin ta kasa da kasa ta (PCUSA) a takaice wanda kuma ke lura da harkokin zuba jari na wanan Chochi,ya furta cewar tuni suka dauki matakin da suka ya dace na dakatar da zuba jari a kamfanonin dake goyon bayan manufofin gwamnatin Isra’ila.

Kungiyar dai ta manyan limaman Chochi ta duniya reshen Amurka,ta baiyana cewar nan da watan gobe zata gindayawa kamfanonin dake hulda da Isra’ila sharu da tilas sai sun cika su kafin su zuba jarin su a irin wadanan kamfanoni.

Bugu da kari Reverend William,yayi nuni da cewar taimakon da wasu kamfanonin na kasahen duniya ke baiwa Isra’ila na kasara dukanin yunkurin da aka sanya a gaba na tabatr da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Palasdinawa.

Chochin dai ta PCUSA ta manyan limaman Chochi na duniya sun zuba jarin su a manyan kamfanonin na kasahen duniya da ya tasama dola biliyan takwas,ciki kuwa har da kamfanonin dake aiki a Isra’ila.

Shi kuwa Clifton Kirkpatrick baban jami’i a Chochin ta Presbyterian,cewa yayi tuni suka fara tattaunawa da wani kamfanin katapila na Amurka dake kera injinan da sojin Isra’ila ke amfani da su wajen rushe gidajen Palasdinawa,inda a yayin wanan tattauanwa kungiyar ta malaman Chochi ta duniya ta ce zata janye jarinta daga kamfanin na katapila na Amurka,don hakan ya zama matsayin horo saboda yadda suke goyon bayan yadda Isra’ila ke kai hare hare kann Palasdinawa.

Bada jimawa bane aka bada labarin cewar wani dan Amurka mai kishin zaman lafiya,shi da wasu kungiyoyi na yahudawa suka kadamar da kamfai na adawa da manufofin kamfanin katapila na Amurka,saboda a shekara ta 2003 sai Rechel Corrie mai kishin zaman lafiya yar asalin Amurka ta rasa ranta a lokacin da katapilar rusa gidaje ta kashe ta a lokacin da ta gudanar da zanga zangar nuna rashin amincewa da rusa gidajen wasu Palasdinawa.

 • Kwanan wata 21.10.2004
 • Mawallafi Jamilu sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvfK
 • Kwanan wata 21.10.2004
 • Mawallafi Jamilu sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvfK