1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Sauyi a Afirka

Kungiyar kwallon kafa ta mata a Sudan

A Sudan an samu wata kungiya ta mata zalla da ke horas da mata wasan kwallo da zimmar zaburar da hazakar sauran mata da ke da sha'awar wasan kwallon kafa da nufin kawo sauyi ga rayuwarsu.

Wasu mata su 15 sanye da kayan wasa na atisaye cikin rana da kura a filin wasa da ke Khartoum babban birni  kasar Sudan. Duk da cewa dai ba kasafai mata ke samun damar irin wadannan wasanni a kasashen Larabawa ko kasashen Musulmi ba, amma wadannan mata na jan daga dan karawa da kungiyar kwallon kafa ta maza.

Sara Edward, ita ce jagorar kungiyar kana mai horas da kungiyar Challagenge team. Ta kuma bayyana irin tunanin sauran mutanen Sudan a kan mata da ke taka leda a aksar.

"Al'ummarmu na tunanin  wasan kwallo na maza ne kadai, a tunanin su duk macen da ke kwallo tamkar namiji ne, ko kuma kawai sai girki da sauran aikace-aikacen gida. Wannan shine kallon da ake mana.”

Duk da rashin samun wani tallafi na musamman, wadannan mata dai na haduwa sau uku a mako, amma farfajiyar da suke taka ledar na cike da duwatsu da ramuka. Sara da ke zama Keptin na kungiyar na cewa babbar kalubalen su shine rashin samun tallafi daga kungiyar kwalaon kafa kasar Sudan.

" Suna samun tallafin kudade daga hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA. Amma idan muka kai musu koken mu na kayan wasa ko filin wasa sai su yi amshin jeka na yi ka ba tare da ganin haske ba.”

Shekarun baya dai, kungiyar kwallaon kafa ta Sudan ta yi alkawarin dubban dalolin dan raya jaririyare kungiyar matan, amma haryanzu gafa sa ne ba tare da ganin alamaun kaho ba. To sai dai a wannan gabar da alama kakar su za ta yanke saka, inda FIFA ta ba da umarnin tura tawagar mata fafatawa a wasannin cin Kofin Afirka na bana.

 

Sauti da bidiyo akan labarin