Kungiyar kasashen Musulmi OIC tayi kira ga dakatar da zubda jini a Iraqi
November 25, 2006A halin da ake ciki kuma kungiyar kasashen musulmi ta duniya tayi kira da dakatar da zubda jini tsakanin yan sunni da yan shia a Iraqi,tana mai tunatarwa shugabannin addini na kasar alkawura da suka dauka na hana zubda jinin musulmi.
A daya hannun kuma wani jamiin kungiyar kasashen larabawa a birnin Alkhahira yace ana sa ran ministocin kasashen wajen kungiyar mai membobi 22 zasu gana a birnin Alkhahira a ranar 5 ga watan disamba inda zasu yi kira ga bangarorin dake yaki da juna a Iraqi dasu kawo karshen yawan zubda jini a kasar.
Sakataren kungiyar kasashen musulmi Ekmaleddin Ihsanoglu yace ya kamata shugabbanin addini na Iraqi wadanda sukayi rantsuwa a dakin Kaaba ba zasu zubda jinin yan uwansu musulmi da suji tsaron Allah su dakatar da wannan balai.
A dai ranar 20 ga watan oktoba ne shugabanin addinin na Iraqi sukayi kira ga magoya bayansu da su dakatar da fada tsakaninsu.