Kungiyar kasashen larabawa ta baiyana goyon bayanta ga shugaba Mahmud Abbas | Labarai | DW | 16.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar kasashen larabawa ta baiyana goyon bayanta ga shugaba Mahmud Abbas

Kungiyar kasashen larabawa tayi alkawarin bada cikakken goyon bayanta ga shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas biyowa bayan kame zirin Gaza da yan kungiyar Hamas sukayi.

Wajen wani taron gaggawa a birnin Alkahira ministocin kungiyar ta larabawa sun yanke shawarar kafa wata hukuma da zata gudanar da bincike akan rikici tsakanin Hamas da Fatah.

Abbas dai ya rushe gwamnatin hadakar ya kuma nada tsohon ministan tsaro Salam Fayyad dan siyasa mai zaman kansa ya jagoranci gwamnatin.

Yan kungiyar Hamas dai suna ci gaba da gangami a Gaza yayinda yan fatah suke rike da yankin yammam da gabar kogin Jordan.

Kungiyar agaji ta Red Cross tace rikicin yankin ya halaka akalla mutane 100 daruruwa kuma suka samu raunuka.