1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar IS ta sace mutane da dama a Siriya

Salissou BoukariAugust 7, 2015

Bayan da ta yi nasarar kwace birnin Qaryatain da ke kasar Siriya, kungiyar IS ta sace mutane a kalla 230 da suka hada da 'yan Sunni da kuma Kiristoci, bisa zargin hada baki da gwamnati.

https://p.dw.com/p/1GBk0
Hoto: Propagandavideo Islamischer Staat via AP

Mutanen dai da suka hada da 'yan sunna 170 da kuma Kiristoci 60 an kame su ne bayan wani bincike da 'yan kungiyar suka aiwatar a gidajansu, inda suke zarginsu da hada baki da gwamnatin ta Siriya a cewar Rami Abdel Rahmane darektan kungiyar da ke kula da sa Ido kan hakokin Bi'adama a kasar ta Siriya.

Sai dai daga na shi bangare Arch-Bishop Matta al-Khoury, da ke birnin Damascus, ya ce basu da wannan labari, amma kuma ya ce suna da masaniyar cewa, bayan da 'yan jihadin na IS suka shiga wannan gari, sun hana kowa fita daga gidansa, domin al'ummar garin ta kasance garkuwa garesu daga harin dakarun gwamnatin ta Siriya.