Kungiyar IS ta dauki alhakin harin London | Labarai | DW | 23.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar IS ta dauki alhakin harin London

A cewar Firaminista May mutumin da ya kai harin da mota dauke da wuka kafin daga bisani jami'an tsaro su aika shi lahira, haifaffen Birtaniya ne.

Firaministar kasar Birtaniya Theresa May a wannan rana ta Alhamis ta gabatar da wani jawabi mai zafi a gaban 'yan majalisar Birtaniya inda ta ce babu wani abu da zai firgita su bayan harin da aka sami wani da kaiwa a gaban harabar majalisar dokokin kasar, Ta ce abun da ya faru a ranar Laraba hari ne na ta'addanci da ke da buri na rufe musu baki a fagen siyasa, kuma ga shi a wannan rana sun koma majalisa.

A cewar Firaminista May mutumin da ya kai harin da mota dauke da wuka kafin daga bisani jami'an tsaro su aika shi lahira, haifaffen  Birtaniya ne. Ta kuma yi amfani da wannan dama a madadin al'ummar Birtaniya wajen nuna godiya ga sauran kasashen duniya da ke ci gaba da mika sakon jaje ga kasar. Kungiyar IS dai ta fito da wasu bayanai a wannan rana inda ta ce maharin na London daya ne cikin sojojinta.