Kungiyar Human Rights Watch ta zargi gwamnatin Sudan da hannu a rikicin Darfur | Labarai | DW | 12.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Human Rights Watch ta zargi gwamnatin Sudan da hannu a rikicin Darfur

Kungiyar kare hakokin bani adama, ta Human Rights Watch, ta zargi hukumomin Sudan, hadda shi kann sa shugabankasa, Omar Hasan El Beshir, da rura wutar rikicin Darfur.

A cikin wani rahoto da kungiyar ta hiddo a yau litinin, ta sannar cewa, kissan kiyasu da ke wakana, da kuma fayde, da ake wa wa mata, hukumomin kasar su ka daure wa, masu aikata su gindi.

Kungiyar, ta yi kira ga komitin Sulhu na Majalisar Dinki Dunia, da kasashe masu hannu da shuni ,da su dauki mattakai kwarara domin hukunta gwamnatin Sudan, domin ko shaka babu, ita ke da babban lefi, a cikin wannan al´amari.

Kazalika ta bukaci kotun kasa da kasa, ta Birnin Hage, ta gudanar da bincike ta kuma gurfanar da sojoji da ta samu da hannu, a ciki, tare da magabantar kasar Sudan.

Ba da wata wata ba gwamnatinSudan ta maida martani ga wannan zargo wanda a cewar ta rahoron na Human Rights Watch ba shi da tuce balle makama.

A cikin sanarwa da ta hido gwamnatin Khartum, ta ce ba ta da alaka ko mua´mila, da yan janjawid, masu yaki da yan tawayen yankin Darfur.