Kungiyar Hamas tayi barazanar kaddamar da Intifada | Labarai | DW | 25.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Hamas tayi barazanar kaddamar da Intifada

Shugaban kungiyar Hamas Khaled Mashaal yace kungiyarsa a shirye take bada waadin watanni shida ga tattaunawar zaman lafiya ta cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin Palasdinu a yamma da kogin Jordan da kuma Gaza,amma tayi barazanar sake kaddamar da tarzoma muddin dai tattaunawar bata samu nasara ba.

Mashaal yana tattaunawa da jamian kasar Masar wadanda suke shuiga tsakani game da batun sojan Israila da aka sace da kuma kafa gwamtanin hadaka tsakanin Hamas da Fatah.

Yace wannan dama ce da ya kamata ayi anfani da ita wajen tabbatr da kasar Palasdinu bisa iyakokin na farko tun watan juni na 1967.