Kungiyar Hamas tace zata kalubalanci kuriar raba gardama
June 11, 2006Talla
Kungiyar Hamas dake mulkin yankin Palasdinawa tace ta shirya kalubalantar shugaba Mahmud Abbas a gaban majalisa gobe litinin idan Allah ya kai mu,dangane da kuriar raba gardama da ya kira a gudanar,kan manhajar kasancewar kasar Palasdinu da Israila kafada da kafada.
Mahukuntan Hamas sunce majalisar dokokin zata gudanar da taron gaggawa gobe litinin,inda zasu mika shawarar gudanar da kuria a majalisar ta amincewa da kuriar ta raba gardama.
Kungiyar Hamas itake da rinjaye a majalisar mai bi mata kuma sai kungiyar Fatah ta shugaba Abbas wadda ta sha kaye a zaben watan janairu.
Shugaba Abbas dai yace yana da ikon kiran kuriar raba gardamar karkashin dokokin yankin Palasdinu.