1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Hamas ta karbi ragamar mulkin yankin Palasdinawa

March 29, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3j

A yau kungiyar Hamas ta karbi ragamar mulkin yankin Palasdinawa,yayinda shugaba Mahmud Abbas ya rantsar da majalisar zartaswa mai membobi 24,ciki har da ministoci 14 da suka taba zaman kurkukun Israila.

Kungiyar Hamas dai tace ba zata canza raayinta game da Israila ba,ana shi bangare mukaddashin firaministan Israila Ehud Olmert yace muddin dai Hamas bata sassauto daga wannan matsayi nata ba,to fa shi da kansa zai sake shata iyakokin Israila tare da mamaye yankuna da dama na Palasdinawa a yamma da gabar kogin Jordan.

Yanzu haka dai hukumar Palasdinawa tana fuskantar matsalolin kudin taimako daga kasashen ketare,inda tuni Israila ta dakatar da bata miliyoyin daloli da take bata a kowane wata.

Kakakin maaikatar harkokin wajen Israila Mark Regev yace a mako mai zuwa majalisar zartarwar Isaraila zata sake duba wasu kafofin karawa hukumar Palasdinawan takunkumi.