Kungiyar hadin kan Turai da kasashen Afirka | Zamantakewa | DW | 21.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Kungiyar hadin kan Turai da kasashen Afirka

Kungiyar hadin kan Turai tayi nazarin yadda zata fuskanci taron koli da kasashen Afirka a Lisbon a watan Disamba

default

Peter Mandelson

Taron kolin da ake shirin gudanarwa tsakanin kungiyar hadin kan Turai da Afirka a Lisbon da kuma yadda hadin kai zai kasance nan gaba, tsakanin kungiyar hadin kan Turai da kasashen ACP da Afirka da Caribien da Pacific sune manmyan al’amuran da aka maida hankali kansu lokacin wani taro yau da ministocin taimakon raya kasashen ketare da kungiyar ta EU suka yi a Bruessels.

Kungiyar hadin kann Turai a nata bangaren tana ganin yanzu dai babu sauran wani abin da zai hana a gudanar da taron kolin da aka shirya cikin watan Disamba tsakanin shugabannin gwmnanatocin kungiyar hadin kann Turai da takwarorin su na kasashen Afirka a Lisbon. Kasar Portugal dake shugabancin kungiyar hadin kann Turai a yanzu, ita ce ta gaiyaci shugabannin wannan kungiya da na kasashen Afirka zuwa ga halartar taron kolin na Lisbon, wanda shine na biyu irin sa, bayan wanda aka yi a shekara ta 2000. Cikin wadanda aka gaiyata har da shugaban Zimbabwe Robert Mugabe, mutumin da kasashen Turai suke ta takaddama a kansa, saboda manufofin mulkin sa na kama karya. Saboda haka ne Pirayim ministan Ingila, Gordon Brown yace ba zai halarci taron kolin na Lisbon ba, idan har Mugabe zai kasance a zauren wanan taro. A daura da haka, shugabannin kasashen kudancin Afrika suna matsa lambar cewar wajibi ne a gaiyaci Mugabe wurin taron. A rdaya hannun, zasu amince a lokacin taron a tattauna a game da batun keta hakkin yan Adam a Zimbabwe, kamar yadda ministan taimakon raya kasaashen ketare, ta Jamus, Heidemarie Wieczozek-Zeul ta fadi a Bruessels. Tace:

Gaba dayan mu, muna bukatar ganin wannan taron koli ya sami nasara. Bayan shekaru bakwai, lokaci yayi da za’a kira irin wannan taro. Za’a tattauna dukkanin al’amura, masu dadi da marasa dadi, amma yana da muhimanci wannan taron koli a yi shi, yadda zam,u tsara manufofi na bai-daya.

Kasashedn Afirka da na kungiyar hadin kann TUrai suna bukatar bullo da wani tsari ne game da raya nahiyar ta Afrika. Ga kasashen Turai, wani bangare na wannan tsari kuwa, shine gabatar da sabuwar yarjejeniyar tattalin arziki da hadin kai tsakanin kungiyar EU da kasashen Afirka da Caribien da Pacific, wato kasashen ACP a takaice. A bisa tsarin da hukumar ciniki ta duniya, wato WTO tayi, shawarwarin neman cimma wannan yarjejeniya kamata yayi a kammala su kafin karshen wnanan shekara., to amma hakan ba zai yiwu ba, saboda kasashen masu tasowa sun ki karbar sharuddan da kasashen na TUrai suka shimfida.

Kwamishinan ciniki na kungiyar hadin kann Turai Peter Mandelson yayi wa kasashen na ACP tayin shigar da klayaiyakin su cikin kungiyar ba tareda haraji ba, tareda taimako, idan har kasashen na Afrika snanu a hankali suka bude kasuwannin su ga kayaiyakin Turai, ko kuma musmman, suka rage abubuwan dake hana ruwa gudu a fannin ciniki tsakanin su kansu. Ministan taimakon raya kasashen ketare ta Jamus, Heidemarie Wieczorek-Zeul tace bata bukatar nuna wani mai laifi a game dfa rashin samun nasarar cimma yarjejeniyar ta hadin kann tattalin arziki da ciniki.

Duk da haka, wajibi ne hukumar kungiyar hadin kann Turai tayi hankali bisa ganin cewar shawarwarin kasashen na Turai da na ACP bai tsaya ga fannin ciniki kadai ba, amma musamman ya kuma shafi fannin taimakon raya kasa, inji Frau Wieczorek-Zeul. A yanzu dai za’a nemi wata yarjejeniya ce ta wucin gadi tare da kasashe da dama na Afirka da Caribien da Pacific, domin tabbatar da ganin akalla a shekara ta 2008 ma, wadannan kasashe masu tasowa sun ci gaba da shigar da kayaiyakin su zuwa kungiyar ta hadin kann Turai.

Wani al’amarin mai muhimanci da ministocin na kungiyar hadin kann TUrai suke son a duba lokacin taron kolin na TUrai da Afrika a watan Disamba, shine fyade da akai ta yiwa mata masu yawa a yankin Kivu dake gabashin Kongo. Dangane da haka, ministan Wieczorek-Zeul take cewa:

Ko kadan kasashe da kungiyoyin duniya ba zasu yarda a ci gaba da samun fyade ko gwada karfi kann kmata a yankin na KIvu ko wasu yankuna da basu da hukumomi ko mahukunta masu karfi a nahiyar ta Afrika ba. Zamu yi iyakacin kokarin mu, domin kare wadannan mata da ga matakai da gwada karfi a kansu.

Frau Wieczorek tayi kira ga gwmanatin Kongo ta dauki matakin hukunta wadanda suke da laifukan yaki da fyade ga mata a kasar.