1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar hadin kan larabawa ta nuna adawa ta matakin komitin sulhu a kan Syria

October 27, 2005
https://p.dw.com/p/BvNk

Kungiyar hadin kan larabawa ta bayyana adawa da matakin ladabatarwa da komitin sulhu na MajalisarDinkin Dunai ke shirin dauka a game da kasar Syria, a sakamakon binciken da a ka gudanar a kan mutuwar tsofan praministan Labanon Raffik hariri.

Idan ba a manta ba, komitin da Majalisar ta girka, ya gano cewar hukumomin Syria na da hannu dumu dumu a cikin kissan gillan.

Syiria kwata kwta ta mussanta wannan zargi, ta kuma sanar cewa za ta girka nata komiti domin ya binciki al´amarin.

Komitin Sulhu na Majalisar Dinkin Dunia mussaman Kasashen Amurika da Fransa, sun bukaci daukar matakan cilastawa hukumomin Syria, bada hadin kai ga masu binciken ta hanyar saka takunkumin karya tattalin arziki.

Sakatare Jannar na kuniyar hadin kan larabawa ya ce sam ba za su amince ba da wannan matakin na rashin adalci da komitin ke shirin dauka a kan Syria.

Kasar Rasha da ke da dangata ta kut da kut da Syria ta bayyana hawan kujera naki, mudun komitin suhlu ya nace da sai ya dauki mataki a kan Syria.