1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar gamayyar Turai ta yaba da capke Hissen Habre

Sakataran kungiyar gamaya Turai mai kulla da taimakon raya kasa, Luis Mishel, yayi lalle marhabin da matakain tsaida tsofan shugaban kasar Cadi Hissen habre da kotu ta yi jiya a kasar Senegal.

Wannan mataki, zai zama na a ba gawa kashi, don mairai ya ji tsoro, ga dukkan shugabanin Afrika da na sauran kasashen dunia, da a zamanin mulkin su, ke nuna azaba ga al´umomin su.

Tun ranar 19 ga watan satumber ne da ya wuce, Kotu a kasar Belgium ta bukaci a gurfanar da Hissen Habre domin zartas masa, da hukunci a game da kissan kiyasu, da su ka wakana kan jama´a zamanin sa.

Nan da dan lokaci mai zuwa, kotun kasar Senegal, za ta yanke hukunci a kan batun dassa keyar Hissen Habre a kasar Belgium.