Kungiyar G8 tayi kira da kawo karshen musayar wuta a gabas ta tsakiya | Labarai | DW | 16.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar G8 tayi kira da kawo karshen musayar wuta a gabas ta tsakiya

Shugabannin kasashe 8 masu arzikin masanaantu G8 sunyi kira da kawo karshen matakin soji da Israila ta dauka a yankin gabas ta tsakiya da kuma karshen jefa rokoki cikib Israilan.

Cikin wata sanarwa da suka amince akai yau,bayan wani taron gaggawa akan rikicin gabas ta tsakiya,shugabannin sun kuma bukaci yan gwagwarmaya dasu maida sojojin Israila da sukayi garkuwa da su tare kuma da sake ministoci da yan majalisar Palasdinawa da Israila ta kame.

Kungiyar ta kuma bukaci majalisar dinkin duniya data duba yiwuwar aikewa da jamian tsaro da kuma masu sa ido zuwa kasar Lebanon.