1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar EU zata ba da taimakon kirkiro aikin yi a Afirka

Kungiyar Tarayyar Turai ta kuduri aniyar samar da guraben aikin yi a nahiyar Afirka a wani mataki na shawo kan matsalar kwararar bakin haure zuwa Turai. Kwamishina shari´a na kungiyar EU Franco Frantini ya nunar da cewa an ware kudi euro miliyan 40 a matakin farko na wannan shirí. Ya ce kasashen Afirka ta Yamma zasu fi cin gajiyar shirin na kirkiro wuraren aiki a Afirka. A lokaci daya kuma hukumar kungiyar EU na duba hanyoyin inganta shigar baki ta hanyoyin da suka dace a cikin kasashe membobinta. A dangane da haka mista Fratini ya ba da shawarar kafa wata cibiyar tsugunar da bakin wadda a gaba zata rika shiryawa bakin hanyoyin samun aiki a Turai.