Kungiyar EU tace a baiwa jamian sa ido katuann izni a Najeriya | Labarai | DW | 13.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar EU tace a baiwa jamian sa ido katuann izni a Najeriya

Masu sa ido na Kubgiyar Taraiyar Turai a zaben Najeriya sunyi kira ga gwamnatin Najeriya data gagauta samarda katunan iznin sa ido a zaben ga masu sa idon,wadanda har yanzu ba su samu katiann ba saoi kadan kafin fara zaben.

Kungiyar ta turai tace ya kamata hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta tayi maza ta baiwa kowace kungiya katuna da take bukata domin basu damar aikewa da masu sa ido ga zabukan da zaa gudanar.

Sai dai kuma a farkon wannan mako shugaban hukumar zabe ta Najeriyar yace yan adawa suna anfani da masu sa ido na cikin gida domin su tarwatsa harkokin zaben.