Kungiyar EU ta yi sassaucin kudin fito a kayan noma | Labarai | DW | 28.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar EU ta yi sassaucin kudin fito a kayan noma

Kungiyar tarayyar turai ta yi sassaucin kashi 46 cikin dari na kudin fito akan kayan noma domin kawo karshen rikicin da ya dabaibaye muhawara a kungiyar ciniki ta duniya ta samun manufar ciniki ta bai daya. Bugu da kari Kungiyar ta kuma yi alkawarin yin ragi mai gwabi na kimanin kashi 60 akan kudin fiton tare dage dukkan rangamen da take bayarwa akan amfanin gona da ake fitar da su zuwa kasashen ketare idan sauran kasashe suka yi makamanciyar wannan yunkuri a yayin taron kungiyar cinikin ta duniya wanda zai gudana a watan Disamba mai zuwa. Kwamishinan ciniki na kungiyar tarayyar turan Peter Mandelson ya baiyana rangamen da cewa zai bude huldodi na kasuwanci da kuma daidaituwa ta fuskar cinikin kayan amfanin gona. Har yanzu dai akwai rarrabuwar kawuna a tsakanin wakilan kungiyar cinikin ta duniya a game da shirin ciniki na bai daya domin bunkasa harkokin kasuwanci da kasashe matalauta.