1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar EU ta kira taron gaggawa a kann yaduwar cutar murar tsuntsaye

October 18, 2005
https://p.dw.com/p/BvOv

Ministocin harkokin waje na Kungiyar tarayyar turai zasu gudanar da taron gaggawa a yau Talata a dangane da yaduwar cutar murar tsuntsaye. Kungiyar tarayyar turan ta sanar da cewa zata haramta shigo da naman kaji daga kasar Girka sakamakon gano bullar cutar murar tsuntsayen a wannan yanki. A cikin wata sanarwa, kungiyar tarayyar turan ta ce tuni kasar girka ta amince da takaita safarar naman kaji daga tsibirin Chios a matakin riga kafi. Kungiyar ta ce tana fatan samun sakamakon bincike na gwajin da likitocin dabbobi suka yi a yankin nan ba da jimawa ba.