Kungiyar EU ta fara yunkurin yin sulhu a Gabas Ta Tsakiya | Labarai | DW | 12.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar EU ta fara yunkurin yin sulhu a Gabas Ta Tsakiya

Bayan da kwamitin sulhun MDD ya amince da kudurin kawo karshen yakin Lebanon, KTT ta fara wani yunkuri yin sulhu a wannan yanki mai fama da rikici. Tun a jiya babban jami´in diplomasiyar kungiyar Javier Solana ya isa a birnin Beirut inda ya gana FM Lebanon Fouad Siniora. Yayin da yake tofa albarkacin bakin sa game da kuduri Solana cewa yayi. Solana ya ce:

„Na gamsu kwarai da amincewa da wannan kuduri. Ina fata sassan biyu zasu amince da shi. A jiya da yamma na gana da FM Siniora da sauran wakilan gwamnatin Lebanon. A yau majalisar ministoci zata yi zama inda na ke fata zata albarkaci kudurin. Sannan ita ma gwamnatin Isra´ila zata tattauna akan kudurin a gobe lahadi inda na ke fata ita ma zata nuna amincewarta. Bayan nan ina fata zata fara janyewa daga Lebanon don a samu tsagaita wuta mai dorewa.“

A wani lokaci yau din nan Solana zai je Isra´ila inda zai yi kokarin shawo hankalin gwamnati don ta amince da kudurin.